2015: Wakilan Turai na ganawa da Buhari

Hakkin mallakar hoto apc
Image caption Buhari zai fafata da shugaba Jonathan

A Najeriya, dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, yana can yana ganawa da wakilan Tarayyar Turai.

Ana ganawar ne dai a yayin da ya rage kwanaki hudu a gudanar da zaben shugabancin kasar.

Majiyoyi sun ce wakilan Tarayyar Turan na bukatar Janar Buhari ya yi kira ga magoya bayansa su kada kuri'unsu cikin lumana, kana su guji tayar da rikici a lokacin zaben.

Rahotanni na cewa ranar Litinin ma dan takarar na jam'iyyar APC ya gana da shugaban kungiyar ECOWAS, John Mahama inda suka tattauna game da zaben na 2015.

Za a yi fafata wa mai zafi a zaben ne tsakanin shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP, wanda ke neman wa'adi na biyu, da Janar Muhammadu Buhari, wanda sau hudu ke nan yana yin takarar shugabancin kasar.