Za a ci gaba da raba katin zabe — INEC

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption INEC ta ce ta gamsu da yadda aka yi rabon

Hukumar zabe a Najeriya ta ce duk da cewa ta kawo karshen rarraba katin zabe a duk fadin kasar, amma za a ci gaba da aikin raba katunan bayan zaben 2015.

Sai dai hukumar ta ce za a ci gaba da raba katin zaben a wuraren da ba a kai musu katin a kan lokaci ba.

Hukumar ta ce da wuya yanzu ta fadi adadin katunan da aka raba sai bayan ta tattara wasu alkaluma.

A baya bayan nan an ruwaito hukumar na cewa ta raba katin sama da miliyan 56 daga cikin sama da miliyan 68, wanda hakan ke nufin akwai kusan katuna miliyan 12 da ba a raba.

Hukumar ta ce ta gamsu da yadda rabon katin ya kasance a fadin kasar.