Zabe: PDP ta mayar wa Buhari martani

Hakkin mallakar hoto AFP AP
Image caption Jonathan na zawarcin masu kada kuri'a

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta mayar wa dan takarar jam'iyyar adawa ta APC martani game da zargin da ya yi cewa PDP za ta yi amfani da makamai domin razana masu kada kuri'a a ranar zabe.

Janar Buhari ya yi zargin cewa jam'iyyar za ta yi amfani da makamai, sannan ta bai wa wasu mutane kakin 'yan sanda na bogi domin su yi harbe-harbe har a soke zabe.

Muhammadu Buhari ya shaida wa BBC cewa, "Maganganun da suke zuwa wajenmu sun nuna cewa an sayi makamai a wasu jihohi, an dinka kayan soja da na 'yan sanda da za a bai wa mutanen da aka koya musu harbi; lokacin zabe za su zo su yi harbi domin a ce an yi tashin hankali, a soke zabe. Saboda haka duk tsarin da PDP take yi na a soke zabe muna samun labari kuma mu gaya wa 'yan Najeriya."

Sai dai daya daga cikin 'ya'yan kwamitin yakin neman sake zaben shugaba Goodluck Jonathan, Alhaji Jafar Sani Bello Gamawa ya ce zargin da dan takarar jam'iyyar ta APC ya yi, zan ce ne marar tushe.

"Wannan zan ce ne da bai kamata jama'a su saurara ba, saboda Shugaba Goodluck ba ya son fitina, mu ne ke da nasara bama bukatar fitina, su ne ba su ga alamar nasara ba, shi ya sa suke neman tunzura mutane," Alhaji Jafar Sani Bello Gamawa.

Ya kara da cewa "Wadannan kalaman na nuna cewa kada jama'a su yarda da 'yan sanda, idan sun gansu, su dauke su a matsayin sojan gona."

A ranar Asabar ne Shugaba Jonathan zai fuskanci Janar Buhari a zaben da ake ganin zai yi zafi sosai.