An sako Sarki Bukkuyum da aka sace a Zamfara

Image caption Mai martaba, Alhaji Muhammadu Usman.

An sako sarkin masarautar Bukkuyum da ke jihar Zamfara da wasu ‘yan bindiga suka yi awo gaba da shi a makon jiya.

Wasu makusantan Sarkin Bukkuyum, Alhaji Muhammadu Usman sun shaida wa BBC cewa masu garkuwa da Sarkin sun sake shi a wani daji da ke kan iyakar jihar ta Zamfara da kuma Kebbi da tsakarar daren ranar Talata.

Wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza da ya zanta da Sarkin a fadarsa ya ce yana cikin koshin lafiya.

Da yammaci ranar Juma’a ne ‘yan bindigar suka yi awo gaba da sarkin daga wani masallaci da ke daf da fadarsa inda ya yi sallar Maghariba.