A-320: Na'urar jirgi ta lalace — Cazeneuve

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin ya fadi ne a yankin da ke cike da tsaunuka

Ministan cikin gidan Faransa, Bernard Cazeneuve, ya ce na'urar da ke nadar murya a cikin jirgin da ya fadi a kasar ta lalace.

Sai dai duk da haka, Mr Cazeneuve na'urar za ta samar da bayanan da masana kan jirgin sama za su yi amfani da su domin gano dalilin da ya sa jirgin da ya kashe mutane fiye da 150 ya fadi

Yanzu haka dai jirage masu saukar ungulu na yin shawagi a yankin da jirgin ya yi hatsari, yayin da 'yan sanda da masu bincike ke duba tarkacen jirgin na Airbus A-320.

Jami'ai sun yi gargadin cewa za a kwashe kwanaki da dama kafin a gano gawarwakin mutanen da suka mutu a cikin jirgin saboda rashin kyawun yanayi.

Zaman makoki a Spaniya

Jirgin -- mallakin -- Germanwings yana kan hanyarsa ce ta zuwa birnin Duesseldorf daga Barcelona.

Firai Ministan Spaniya, Mariano Rajoy, ya bayyana cewa kasarsa za ta yi makokin kwanaki uku domin tunawa da 'yan kasar su 45 da ke cikin jirgin da ya yi hatsari.