India ta soke wata doka da ta shafi tsokaci a facebook

Hakkin mallakar hoto AP

Kotun Kolin Indiya ta soke wata doka mai cike da kace-nace da ta ke bai wa 'yan sanda damar tsare mutane idan sun yi wasu kalamai a shafukan sada zumunta da kuma wasu shafukan internet

Kotun ta zartar da hukuncin cewa sashen 66A na dokar fasahar sadarwa mai cike da kace- nace ta saba kundin tsarin mulki

A 'yan shekarun nan an kama mutane da yawa saboda wasu kalamai da su ka yi a shafin sada zumunta na Facebook ko Twitter da suka harzuka jama'a

Gwamnati ta kare wannan dokar ta na mai cewa an yi ta ne domin ta hana mutane daga nadar abubuwa masu cutar da wasu

Kamfanin dillacin Labaru na AFP ya ambato mai shari'ah RF Nariman ya na cewa sashen 66A ya saba kundin tsarin mulki kuma bamu da tababar soke shi'

Wannan sashe ya shafi 'yancin mutane na sanin wani abu kai tsaye in ji Alkalin

Wani dalibin koyan aikin lauya ne ya fara kalubalantar wannan doka bayan tsare wasu 'yan mata biyu a watan Nuwambar shekarar 2012 a Mumbai saboda kalaman da su ka yi a shafin sada zumunta da mahawara na Facebook bayan mutuwar wani san siyasa Bal THackery

Jama'a sun harzuka a Indiya bayan an tsare 'yan matan inda da dama suka yi ta kiran a soke dokar

Tun daga wancan lokacin aka rinka samun mutanen da ake tsarewa saboda dokar