Shugabanni sun ziyarci inda jirgi ya fadi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har yanzu ana aikin ceto yankin Alps din Faransa

Shugabannin Faransa da Spaniya da kuma Jamus sun ziyarci tsaunukan nan na Alps na Faransa, inda jirgin saman kasar Jamus ya fadi.

Lamarin ya janyo mutuwar mutane dari da hamsin da ke cikin jirgin.

Ana sa ran za su gana da 'yan 'uwan wadanda hadarin ya halaka.

A halin da ake ciki dai jiragen saman helikwabta suna ci gaba da neman gawawwaki duk da ruwan sama da dussar kankara da aka fara samu.

Ministan cikin gidan Faransa, Bernard Cazeneuve, ya ce na'urar da ke nadar murya a cikin jirgin da ya fadi a kasar ta lalace.

Sai dai duk da haka, Mr Cazeneuve na'urar za ta samar da bayanan da masana kan jirgin sama za su yi amfani da su domin gano dalilin da ya sa jirgin ya fadi.