An yi na'urar gano halayyar zuma

Hakkin mallakar hoto
Image caption Na'urar gano halayyar zuma

Masu nazarin ilimin gano yadda kwari da dabbobi suke rayuwa na yin gwajin na'urar gano dabi'ar zuma, a London.

Dr. O'Neill, injiniya a kamfanin fasaha na Tumbling Dice da ke Newcastle, shi ne yake kirkirar na'urar daga fasahar amya.

Ya ce " kawo yanzu na yi guda 50. Na kuma hade su da teburina-abun dai kamar aikin tiyatar asibiti".

Masu son yin nazari za su ga yanayin halayyar zumar ta kafar amyar wadda ita kuma aka hada ta da na'urar komfuta.