Zabe: Nigeria za ta rufe kan iyakokinta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kan iyakar Nigeria da Kamaru

Nigeria ta sanarda rufe dukkan kan iyakokinta na kasa da na ruwa a yayinda ake shirin zaben shugaban kasa a ranar Asabar.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar a cikin wata sanarwa ta ce daga karfe 12 na daren ranar 25 ga watan Maris zuwa daren ranar Asabar, 28 ga watan Maris kan iyakokin za su kasance a rufe.

Sanarwar ta ce an dauki matakinne saboda a gudanar da zabe cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sanarwar ta kuma umurci hukumar da ke kula da shige da fice ta Nigeria ta tabbatar da cewa 'yan kasashen wajen ba su shiga cikin zaben ba.