An kai hari kusa da gidan shugaban Yemen

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babu tabbas kan inda shugaba Abdul Rabbu Mansur Hadi yake

Jiragen saman yaki a Yemen sun harba makamai masu linzami a wata unguwa a kudancin garin Aden inda a nan gidan shugaba Abdul Rabbuh Mansour Hadi ya ke.

Ana samun rahotanni masu karo da juna game da wurin da shugaban kasar yake, yayin da 'yan tawaye ke kara yin kofar raggo a birnin Aden mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin kasar, inda shugaban ya mayar da gwamnatinsa.

Amma masu ba shi shawara sun tabbatar da cewa shugaban yana nan lafiya.

Wakilin BBC ya ce lafiyar shugaba Hadi na fuskantar barazana bayan da mayakan Houthis suka kwace wani sansanin soji mai muhimmanci, mai nisan kilomita 40 da garin Aden.

Ministan harkokin waje na Yemen ya yi kira ga kasashen Larabawa akan su turo musu da sojoji da zasu taimakawa kasar.