Nigeria: Mutane na yin kaura zuwa yankunansu

A lokacin da zaben Nigeria ya rage saura 'yan kwanaki, jama'ar kasar da ke zaune a wasu sassa da ba nasu ba, a yanzu haka na ta komawa yankunansu.

Masu tserewar dai na cewa suna kokarin kaucewa tashe- tashen hankula ne irin wadanda suka faru bayan zaben shekarar 2011.

A ranar 28 ga watan Maris za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na 'yan majalisar dokoki

Sai dai manyan 'yan takarar Shugabancin Nigeriar biyu sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar yin zaben lafiya ba tare da tashin hankali ba.