2015: Ranar karshe a yakin neman zabe

Masu gangamin yakin neman zabe Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Masu gangamin yakin neman zabe

Yau Alhamis ita ce ranar karshe ta duk wani yakin neman zaben da 'yan takarar shugaban kasa da na yan majalisun dokoki zasu yi a zaben da za a yi ranar asabar.

Binciken da muka gudanar ya nuna cewar babu wani babban gangami da manya manyan jam'iyyun siyasa na PDP da APC suka shirya yi a wannan rana.

A yayin da a jiya laraba, jam'iyyar PDP ta yi wani taron manema labarai a hedkwatarta da ke Abuja, a yau ake sa ran dan takarar jam'iyyar APC Mohammadu Buhari zai yi nashi tarin da manema labarai.

Saidai a yayin da ake kawo karshen yakin neman zaben, kwamitin nan da ke sa ido wajen tabbatar da an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali na ganawa da 'yan takarar manyan jam'iyyu biyu na kasar Dr Goodluck Jonathan da kuma Janar Muhammadu Buhari.

Kwamitin ya na karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soji na Nigeria, Janar Abdussalami Abubakar da kuma Rev Mathew Kukah.