Ford zai sayar da mota mai gane alamomin hanya

Hakkin mallakar hoto ford

Kamfanin motoci na Ford zai soma sayar da wata mota da zata iya karanta alamomin hanya sannan ta rage gudu idan akwai bukata, domin tabbatar da cewar motar bata gudu sosai

Za a iya kunna wannan fasaha ta takaita gudu ta hanyar sitiyarin motar sannan za'a iya dakatar da ita ta hanyar danne totar din motar

Kamfanin kera motocin ya nuna cewa wannan fasaha zata taimakawa direbobi kaucewa biyan tara sannan zata rage yawan hadurra

Wannan fasaha zata bayyana ga jama'a a watan Agustar shekarar da ake ciki a lokacin da kamfanin Ford zai kaddamar da wasu motocinsa na S-Max a nahiyar Turai

Wani mai magana da yawun kamfanin Ford na Amurka ya fadawa BBC cewa maiyiwuwa za'a sanya wannan fasaha a wasu samfuran motocin a duniya

Ford ya ce a shekarar 2013, fiye da direbobi 15,000 a Burtaniya aka ci tarar kudi da za ta kai ta £100 ko fiye bayan da aka kama su suna gudun da ya wuce kima a inda ya kamata ace sun takaita gudun