INEC ta fara raba kayan zabe ranar Alhamis

Image caption Attahiru Jega, shugaban hukumar INEC

Hukumar zaben Najeriya, INEC ta fara raba kayan zabe zuwa mazabu, ranar Alhamis.

A baya dai hukumar tana raba kayayyakin zaben ne ranar jajiberin zaben, amma wannan karon ta raba kayan kwanaki biyu kafin zaben.

Hakan kuwa INEC ta ce zai kawo karshen isar kayan zaben zuwa mazabun kasar, al'amarin da ke kawo tsaiko wajen gudanar da zaben akan kari.

A daren ranar Laraba ne dai aka rufe iyakokin kasar har na tsawon kwanaki uku masu zuwa, saboda jami'ai sunce an fada musu cewa wadanda ba 'yan Nigeria ba na shirin shigowa domin yin zabe.