Yemen: Ana gab da dakatar da hari kan Houthi

Hakkin mallakar hoto European Photopress Agency
Image caption Za a tsayar da hare-hare kan Houthi

Ministan kasashen waje na kasar Yemen, Riyadh Yasin ya shaida wa BBC cewa hare-haren da suke kai wa 'yantawayen Houthi na kankanin lokaci ne kuma suna dab da karewa.

Ya kuma ce idan dai har hakarsu ta cimma ruwa suka kuma dakile karfin 'yantawayen Houthi, za a iya kammala hare-haren a cikin 'yan kwanaki ko ma 'yan sa'o'i.

Yasin kara da cewa yana fatan shugaban kasar Yemen din , AbdRabbuh Mansour Hadi zai halarci taron koli na kungiyar kasashen Larabawa da ake sa ran gudanarwa a wannan satin.

Sai dai kuma ya ce har yanzu ba su da tabbacin irin illar da hare-haren na sama za su iya yi wa 'yan Houthin, amma ba shi da masaniyar ko akwai yiwuwar yin amfani da dakarun soji akan mayakan idan har al'amarin ya ta'azzara.

To amma an jiyo Jagoran mayakan Houthin, Abdulmalik al-Houthi yana la'antar kasar ta Saudiyya.