Iran ta bukaci a dakatar da hari a kan Yaman

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mayakan 'yan Houthi sun kwace yankunan da dama a Yaman

Iran ta nemi lalle take-yanke a dakatar da hare-haren soji na kasashen Larabawa da Sa'udiyya ke jagoranci a 'yan tawaye Al-Hauthi 'yan Shi'a a Yaman.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana hare-haren jiragen sama da ake kaiwa a kan wuraren Al-Hauthin a matsayin mamaya, kuma mataki ne mai hadari da zai babu abin da zai haifar illa munana rikici na Yaman.

Da ma dai Saudiyyar da sauran kasashen Larabawa sun dade suna zargin Iran din da goyon bayan 'yan tawayen na Al-Hauthi.

Kungiyar kasashen Larabawa ta nuna goyon bayanta kan hare-haren da ake kaiwa mayakan Houthis.

Saudiyya ta ce kasashe fiye da goma ke cikin kawancen da take jogoranta.