Cincirindo a rumfunan cirar kudi a Kano

Image caption atm queue

Yayin da ya rage kwana daya da zaben Nigeria, mutane a jihar Kano da ke arewacin kasar na yin tururuwa domin cirar kudi a na'urar ATM.

Tun daga ranar Alhamis ake samun dogayen layuka a wajen cirar kudin, yayin da suma cikin bankunan suka cika makil da jama'a masu son cira ko kuma aikewa da kudi.

Wakilin BBC da ke Kano wanda ya zagaya wuraren da injinan ATM suke, ya ce mutane kan yi sa'o'i biyu ko ma fiye a kan layi domin kokarin ciro kudin.

"Tun misalin karfe 10 na safe na zo wajen nan amma gashi yanzu har 12 ta yi, layi bai zo kaina ba," in ji Bala wanda yana daya daga cikin masu bin layin.

Mafi yawan mutanen da ke kan layin sun shaidawa BBC cewa matsalar rashin kyawun sadarwa ke jawo cikowar jama'a da kuma bata lokaci.

"Da mutum 2 ko 3 sun ciri kudi sai kaga injin ya tsaya ," in ji Bala.

Cinkoson dai ya ta'azzara ne saboda kasancewar a gobe ne za a yi zabukan kasar wanda zai hana jama'a fita don yin wasu hidimomin.