Boko Haram: Sojoji sun kwato garin Gwoza

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dakarun Nigeria sun kwato garuruwa da dama daga hannun Boko Haram

Rundunar tsaron Nigeria ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kwace garin Gwoza, inda nan ne shalkwatar kungiyar Boko Haram.

Rundunar tsaron ta ce a safiyar ranar Juma'a ta kwace garin inda ta hallaka 'yan Boko Haram da dama sannan ta kama wasu daga cikin mayakan kungiyar.

Kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirarin.

Rahotanni da dama dai sun nuna cewa 'yan Boko Haram na tsare da 'yan matan Chibok fiye da 200 a garin na Gwoza.

Wannan ikirarin na sojojin Nigeria na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya soki hukumomin Nigeria a kan cewar sun bar dakarun Chadi su kadai suna yakar Boko Haram a wasu garuruwan Nigeria.

A hira da Jaridar "Le Point" ta Faransa, Mr Deby a wasu lokuta suna kara komawa garuruwan da suka kwato daga Boko Haram saboda dakarun Nigeria ba su je sun karbi garuruwan ba.