Matukin jirgin da ya yi hatsari na da ciwon damuwa

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Har yanzu ana ci gaba da binciken wasu kayayyakin da Andreas Lubitz ya bari a duniya.

'Yan sanda a Jamus sunce sun gano wasu abubuwa masu mahimmanci, a daya daga cikin gidajen da Andreas Lubitz yake zama, matukin jirgin da ya karkatar da akalar jirgin da yake tukawa cikin tsaunuka.

'Yan sanda basu bayar da cikakkun bayanai ba, game da abinda suka bankado, amma an yi awon- gaba da wasu abubuwa da matukin jirgin yake amfani da su, ciki harda kwamfutarsa domin a yi bincike.

Yayinda binciken ke ci gaba da gudana game da dalilin da yasa Lubitz ya kashe rayuka 150 tare da nasa, an gano cewa dole sai da ya katse horon da ake ,masa na tukin jirgi a shekarar 2008, saboda ya sha maganin cutar da aka yi imanin cewa ta shafi matsananciyar damuwa.

Ministan cikin gida na Jamus ya ce binciken tsaro da aka gudanar bai nuna akwai matsala tattare da shi ba, yayinda kamfanin da yake yiwa aiki na Luftansa, ya jaddada cewa Lubitz nada kwarewa dari- bisa- dari ta tukin jirgi