Na shirya taka leda a Chelsea - Omeruo

Image caption Omerou ya haskaka a wasansa da Super Eagles a 2013

Dan wasan baya, Kenneth Omeruo ya ce ya shirya bugawa Chelsea kwallo idan har ya kamalla zaman aro a Middlesbrough.

Dan shekaru 21, dan wasan Nigeria din ya koma Chelsea ne a watan Junairun 2012, amma tun a watan Junairun 2014 yake a matsayin aro a Boro.

Omeruo ya ce "Na samu gogewa kuma ina jiran lokaci na a gasar Premier a kakar wasa mai zuwa."

Daga kungiyar Standard Liege ya koma Stamford Bridge a kakar wasa ta 2012 zuwa 2013.

Ya bugawa Super Eagles wasanni a gasar cin kofin Afrika a 2013 inda Nigeria ta lashe gasar.