An ci tarar PayPal sama da dala miliyan 7

Hakkin mallakar hoto AP

PayPal ya amince ya biya sama da dala miliyan bakwai ga gwamnatin Amurka bayan ikirarin da aka yi cewa ya bayar da damar biyan wasu kudade da suka saba takunkumin da aka sanyawa Iran da Cuba da kuma Sudan

Ma'aikatar baitulmalin Amurka ta ce kamfanin na biyan kudi ya gaza wajen tantancewa da kuma kare hada- hada ta kudi.

Hadar hadar kudin ta hada da ta dala dubu bakwai daga wani da yake cikin jerin sunayen mutanen da gwamnatin Amurka ta ce yana hannu a bazuwar makaman kare dangi

Sai dai kamfanin PayPal ya ce ya inganta aikinsa

A wata sanarwa da ya fitar, kamfanin ya ce ya bayar da rahoto ga hukumomin da suka dace kan wasu kudade da aka biya da ya aiki akan su tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013

Tsakanin watan Oktobar shekarar 2009 da kuma Afrilun shekarar 2013 an bada rahotan cewa PayPal ya gudanar da wasu hada hada 136 zuwa ko kuma daga wani asusu da aka yi rajistarsa da sunansa

Wasu kudaden da aka biya sun hada da kayayyaki dake tafiya da kuma zuwa kasashen Cuba da Sudan da kuma Iran

Gabakiya kamar yadda Ma'aikatar baitunmalin Amurka ta nuna, kamfanin PayPal ya yi hada hadar kudade kusan 500 da ta sabawa takunkumin da suka haramtawa kamfanonin Amurka daga yin harkokin kasuwanci tare da daidaikun mutane ko kuma kungiyoyi dake cikin bakin littafin Amurka