Ebola: Hukumomi sun killace jama'a a Saliyo

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Har yanzu akwai masu cutar a Saliyo

Hukumomi a Saliyo sun soma tilasta takaita zirga- zirgar mutane ta kwanaki uku, da nufin kawo karshen barkewar cutar ebola a cikin kasar.

Kusan mutane miliyan shida ne aka nemi su zauna a gida har nan da kwanaki uku masu zuwa, yayinda masu aikin sa-kai ke bi gida-gida suna neman mutanen dake dauke da alamomin cutar, da kuma tunatarwa saura akan hanyoyin da zasu bi su kare kansu.

A wannan karon mutane nada damar su dan fita na 'yan sa'oi saboda sallar juma'a sannan kuma zuwa coci a ranar Lahadi

Har yanzu dai ana ci gaba da samun rahotannin samun barkewar cutar ebolan a arewaci da kuma yammacin Saliyo a kowanne mako.

Kasashen yammacin Afirka uku da cutar tayi wa illa da suka hada Saliyon da Liberia da Gini, na fatan ganin cewa ba a sake samun mai dauke da kwayar cutar ba, zuwa tsakiyar watan gobe