Yemen: An sake kai hare-hare kan Houthi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kungiyar kawancen da Saudi ke jagoranta tace tana samun nasara a hare-haren da take kai wa kan Houthis

Jiragen yaki na kungiyar kawancen da Saudi Arabia ke jagoranta sun sake kai manya-manyan hare-haren bama-bamai kan 'yan tawaye na kabilar houthis a Yemen.

An kai harin ne arewaci da kuma babban birnin kasar Sana'a. Jami'an soji sun ce an kai wasu harin ne kai tsaye kan matattarar 'yan Houthis din.

An shafe dare ana ta lugudan wuta a Sana'a. An kashe akalla mutane goma 18 yayinda da dama kuma suke tsarewa daga birnin. Ahmad Bin Hassan Asiri, mai bawa ministan tsaron Saudia shawara ne ya ce suna samun nasara a hare-haren da suke kaiwa kan 'yan tawayen.

Ya ce "mun fara ganin sakamakon hare-haren da muke kaiwa tun a mintuna goma sha biyar na farko, muna kuma kara samun nasara." Ana samun nasarar hare-haren saboda anyi amfani da jiragen yaki masu yawa.

Ministan kasashen waje na kasar ta Yemen, Riyadh Yasin ya shaida wa BBC cewa hare-haren da suke kai wa 'yan tawayen Houthi na kankanin lokaci ne kuma suna dab da karewa. Ya kuma ce idan dai har hakarsu ta cimma ruwa suka kuma dakile karfin 'yan tawayen Houthi, za a iya kammala hare-haren a cikin 'yan kwanaki ko ma 'yan sa'o'i.