Zabe: 'Yan Nigeria sun yi fitar-dango

Image caption Mata sun fito da dama a jihar Kaduna

Rahotanni daga sasa daban-daban na Nigeria sun ce miliyoyin mutane sun fito kwansu da kwarkwartasu domin kada kuru'unsu.

Amma a wurare da dama, an fuskanci jinkiri wajen kai kayan zabe, yayin da kuma a wuraren da kayan zaben suka je, an fuskanci matsaloli musamman da na'urar nan mai tantance masu zaben, ko da yake daga bisani an gano kan matsalar kuma abubuwan sun fara tafiya kamar yadda ake so.

Wasu kungiyoyin kasashen waje da ke sanya idanu a zaben na Najeriya sun ce sun lura da cewar an samu matsaloli da jinkirin fara aikin zaben a wurare da dama a babban birnin tarayyar Najeriyar Abuja da ma sauran sassan kasar.

Tun da farko da safiyar ranar zaben hukumar zaben Najeriya ta sanarda dage zaben 'yan majalisar wakilai na dukkan mazabu a jihar Jigawa bisa dalilan rashin kayan aiki.

Shugaban hukumar zaben na jihar ta Jigawa sai da ya sanar da dage zaben 'yan majalisun tarayyar na mazabu takwas kafin daga bisani ya kara da sauran mazabu uku.