Google ya yi rashin nasara a shari'a

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Google ya fadi a shari'a

kamfanin matambayi baya bata na Google bai samu nasara a shari'ar da ya nemi kotu ta hana abokan huldarsa yin karar kamfanin bisa zarginsa da yin kutse ga sirrin masu amfani da shi.

Wani gungun masu amfani da tsarin intanet na Google din ne suka zargi kamfanin da yi musu kutse cikin sirrinsu ta kafar 'safari'.

Kamfanin dai ya bayyana rashin jin dadinsa da yanke shari'ar da kotun tayi.

Sai dai kuma wani daga cikin wadanda suka kai karar ya bayyana nasarar da suka samu da wata gagarimar nasara.