Boko Haram:An kashe dan majalisar dokokin Gombe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya-bayan nan ne kungiyar Boko Haram ta sha alwashin kai hare-hare a lokacin zabukan Nigeria

Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane akalla 22, ciki har da wani dan majalisar dokokin jihar Gombe daga yankin Dukku.

Maharan sun kai hare-haren ne da bindigogi a wasu kauyuka dake kananan hukumomin Nafada da Dukku da kuma Funakaye lokacin da ake tantance mutane.

Wakilin BBC ya kuma ce mutane da dama sun jikkata, yayin da jama'a suka shiga cikin zulumi.

Lamarin dai ya faru ne a kauyukan Bolawa da Birin Fulani inda aka kashe mutune uku har da dan sanda daya, yayin da a kauyen Shole dake karamar hukumar Funakaye ma aka samu asarar rayuka amma dai daga bisani an ci gaba da zabukan.

A baya dai, kungiyar Boko Haram dake gudanar da ayyukanta a jihohin arewa maso gabashin Nijeriya, ta yi barazanar dagula zabukan Najeriya, kafin dakarun tsaron kasar da na kasashen da ke makwabtaka kamar Kamaru da Nijar da Chadi suka karya lagonsu, cikin makwanni 6 da aka dage zabukan.