Nigeria: An dage zabe a wasu wurare

Hakkin mallakar hoto b
Image caption An fuskanci matsala wajen tantance mutane da dama

Hukumar zaben Nigeria- INEC ta dage zabe a wasu yankuna da aka fuskanci matsala wajen yin aiki da na'urar tantance masu kada kuri'a.

Hukumar ta tabbatar cewa an fuskanci matsaloli wajen yin amfani da na'urorin na card reader, don haka za a yi zabe a wauraren.

Sai dai hukumar ba ta bayyana yawan wuraren da aka fuskanci wannan matsala ba.

Kwamishinan hukumar, Chris Yimoga, ya shaida wa manema labarai cewa za a gudanar da zabe ranar Lahadi a wuraren da suka fuskanci matsalar.

Shi kansa shugaban kasar, Goodluck Jonathan, ya fuskanci matsala kafin a tantance shi, domin kuwa sai da aka yi amfani da card reader hudu domin tantance shi, kuma duk da haka ba su yi aiki ba.