An samu matsaloli wajen tantance mutane a Nigeria

Image caption Mutane sun fito kwansu da kwarkwatar su, domin su kada kuri'a.

Rahotanni daga jihohin Filato da Bauchi da Gombe, da Taraba da Yobe da Borno da kuma Adamawa na cewa tun da sanyin safiya mutane suka yi dafifi a mazabunsu domin a tantancesu don su samu damar kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki na tarayya.

Mutane, maza da mata, sun fito sosai da sosai, wasunsu tun da asubahi inda suka kama layi. A wasu wurare dai aikin ya gudana yadda ya kamata inda aka tantace mutane da dama.

To sai dai bayanai daga mazabu da dama na cewa ba a soma aikin tantancewar a kan lokaci ba, inda a wasu wuraren aka samu jinkirin kimanin sa'o'I biyu zuwa uku, sabo da rashin zuwan ma'aikatan zabe.

Haka-zalika bayanai na cewa na'urar tantance masu zabe watau Card Reader, bata aiki yadda yakamata, a wurare da dama, inda a wasu wuraren bata iya daukar zanen yatsun masu jefa kuri'a, a wasu wuraren kuma bata aiki sam-sam, kana an samu matsalar batir, lamarin kum ya fi Kamari a jihar Filato.

Tuni dai har mutane sun fara kada kuri'unsu a mazabu da yawa da ke jihohin.

Hukumar zabe ta INEC dai ta ce duk wanda na'ura bata amince da zanen yatsunsa ba, za a ba shi wata takarda ya cike, kana a bar shi ya jefa kuri'a muddin dai na'ura ta amince da sahihancin katinsa. Kawo yanzu dai aikin na gudana lami lafiya, yayin da masu jefa kuri'a ke nuna halin natsuwa da bin doka.