An kai hari a Alkaleri, Bauchi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kungiyar Boko Haram sun kashe dubban mutane a arewacin Najeriya.

Rahotanni daga garin Alkaleri na jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun yi ta harbe-harbe ranar Lahadi.

Sai dai har yanzu babu cikakken bayani a kan jikkata ko rasa rayuwa a wannan lamari.

Wakilin BBC a yankin ya ce mazauna garin sun firgita sanadiyar jin karar harbe-harben.

A ranar Asabar ma 'yan bindiga da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane akalla 22, ciki har da wani dan majalisar dokokin jihar Gombe daga yankin Dukku.

Maharan sun kai hare-haren ne da bindigogi a wasu kauyukan da ke kananan hukumomin Nafada da Dukku da kuma Funakaye lokacin da ake tantance masiu kada kuri'a.