Ban Ki Moon ya jinjina wa 'yan Nigeria

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Ban ya ce 'yan Nigeria sun taka rawar gani a wannan zaben

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya taya 'yan Najeriya murnar gudanar da zaben shugaban kasa cikin lumana duk da cewa akwai hare-haren 'yan Boko Haram.

Mr Ban ya yi Allah-wadai da yinkurin 'yan Boko Haram na kokarin dagula zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a jihar Gombe.

A cewarsa 'yan Najeriya sun nuna jajircewa wajen fitowa kwansu da kwarkwata domin kada kuri'a.

Mr Ban ya yi kira ga bangarorin da ke hammaya a zaben sun guji tashin hankali a lokacin tattara sakamako da kuma lokacin da aka sanar da sakamakon zabukan.

An ci gaba da zabe a rana ta biyu na zaben, bayan da aka fuskanci tsaikon na'urar Card Reader.