Sakamakon zabe daga INEC ne kadai sahihi - Jega

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban hukumar zabe a Najeriya Attahiru Jega

A Najeriya, a yayin da 'yan kasar ke dakon sakamakon zabukan ranar Asabar, shugaban hukumar zaben kasar ya nuna damuwa game da yadda wasu ke amfani da shafukan sada zumunta wajen sanar da sakamakon zabe.

A wajen wani taron manema labarai a Abuja, Farfesa Attahiru Jega ya yi gargadin cewa akwai hadari sosai idan jama'a suka ci gaba da bayyana sakamakon zaben da ba hukumar INEC ce ta sanar ba.

Ya ce hukumar zaben tana kokarin ganin an sanar da sakamakon zaben zuwa ranar Talata, domin wasu jihohin har sun kammala hada sakamakon zaben shugaban kasa.

Farfesa Jega ya kuma bayyana gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa dana 'yan majalisar dokokin tarayya, duk da cewa an fuskanci matsaloli da suka sa a ka jinkirta zaben zuwa ranar Lahadi a wasu wurare.