Nigeria: Ana ci gaba da zabe ranar Lahadi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu kada kuri'a a kan layi

A Najeriya, za a ci gaba da kada kuri'a yau a wasu sassan kasar inda matsalolin da suka hana a fara zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki ranar asabar a kan lokaci.

Shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Attahiru Jega ya ce ko da yake hukumar ba ta ji dadin yadda aka ci karo da matasala wajen amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a ba, matsalar ba ta taka kara ta karya ba.

Ya ce matsalar ba zata shafi ingancin zaben ba, domin daga cikin runfunar dubu 119 da ake dasu, a rumfuna 350 ne aka fuskanci matsalar.

Farfesa Jega ya bayyana gaddamar da na'urar ta yi wajen tantance shugaban kasar Goodluck Jonathan a matsayin abin takaici, kuma abin kunya ga kasar.

Jihohin Naija da Lagos suna daga cikin wuraren da za a ci gaba da zabe a yau.