Zabe: An fara yakin neman zabe a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pirayi Ministan Biritaniya David Cameron

An fara yakin neman zabe a Biritaniya a shirye-shiryen da ake yi na gudanar da babban zaben kasar.

Jim kadan kafin tsakar daren Lahadi ne dai aka rushe majalisar dokoki, al'amarin da ya kawo karshen shekaru biyar na gwamnatin hadin gwiwa a tsakanin jam'iyyar Conservative ta David Cameron da jam'iyyar Liberal Democrat.

Jam'iyyar Conservatives ta yi alkawarin cewa idan aka zabe ta za ta gudanar da kuri'ar raba-gardama a kan ci gaba da kasancewar Biritaniya a Tarayyar Turai.

Babban abokin hamayyar Mr Cameron, kuma jagoran jam'iyyar Labour, Ed Miliband, ya yi gargadin cewa shirin da jam'iyyar Conservative ke da shi na gudanar da kuri'ar raba-gardama a kan ci gaba da kasancewar kasar a Tarayyar Turai babban hadari ne ga 'yan kasuwar kasar.

Ana sa ran sarauniyar Ingila za ta yi takaitacciyar ganawa da Firai Minista David Cameron.