Nigeria: Shin wanne hali INEC ke ciki?

Image caption Jega ya ce za a soma bayyana sakamakon da karfe 12 na rana.

Hukumar zaben Najeriya ta ce da karfe 12 na rana a agogon kasar za ta fara tattara sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a karshen makon jiya.

Shugaban hukumar, Farfesa Attahiru Jega, ya shaida wa BBC cewa za su rika bayyana wanda ya lashe zaben ne daki-daki.

A cewarsa za a fitar da sakamakon ne jiha zuwa jiha, inda za a fara daga sakamakon jihar da ya fara zuwa hannunsu.

A karshen mako ne dai aka yi zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki.

Fafatawa ta yi zafi ne tsakanin shugaban kasar, Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP, da Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.