APC na kan gaba a zaben shugaban Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Attahiru Jega

A Najeriya, hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar a jihohi 18 da babban birnin tarayya Abuja.

Jam'iyyar adawa ta APC ce ta lashe zaben a jihohin Kaduna da Kano da Jigawa da Katsina da Ondo da Ogun da Osun da Kogi da Oyo da Kwara.

Ita kuwa jam'iyyar PDP ta yi nasara a jihohin Akwa Ibom da Enugu da Nassarawa da Abia da Ekiti da Plateau da Imo da Anambra da FCT.

Kawo yanzu, jam'iyyar APC ta Janar Muhammadu Buhari ce ke da rinjaye a kan jam'iyyar PDP ta Shugaba Goodluck Jonathan, yayin da kuma ake dakon sakamakon sauran jihohi 18.

Shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Attahiru Jega ya ce a yau Talata ne za a ci gaba da sanar da sakamakon zaben daga sauran johohin