Zabe: An fitar da sakamako a Kano

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumar zaben ta ce APC ce ta yi nasara a Kano inda ta samu kuri'u miliyan daya da dubu dari tara, da dubu uku, da dari tara da casa'in da tara.

Hukumar zaben Najeriya reshen jihar Kano ta fitar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a karshen mako, inda ta bayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta yi nasara.

Baturen zabe a jihar, Farfesa Muhammadu Hamisu, ya ce a cikin masu kada kuri'a fiye da miliyan biyu, jam'iyyar ta APC ta samu kuri'u miliyan daya da dubu dari tara, da dubu uku, da dari tara da casa'in da tara.

A cewarsa, jam'iyyar PDP ce ta zo ta biyu, inda ta samu kuri'u 215,779.

Sai dai wakilin jam'iyyar ta PDP, Akilu Sani Indabawa, ya shaida wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai cewa ba su amince da sakamakon zaben ba.

A cewarsa jam'iyyar tasu za ta fitar da matsayinta a kan sakamakon zaben.

Kwankwaso ya zama dan majalisar dattawa

Haka kuma hukumar zaben ta ce APC ta lashe dukkanin kujerun 'yan majalisar dattijai uku, da kuma na yan majalisar wakilai 24 daga jihar.

Mai tsawatarwa a majalisar dattijai, wanda kuma yake majalisar tun 1999 ya sha kaye a hannun Barau Jibrin, tsohon dan majalisar wakilai daga Kano.

Kazalika gwamnan Jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi nasarar tafiya majalisar dattijai.