Kai Tsaye: Sakamakon zaben Najeriya

Latsa nan domin sabunta shafin

Image caption Shugaban hukumar zabe, INEC Furofesa Attahiru Jega

Barkanmu da warhaka da kuma ziyartar shafin BBC Hausa kai tsaye a kan sakamakon zaben Najeriya na 2015. Miliyoyin 'yan Najeriya sun kagara su sana shugabannin da suka zaba a ranar Asabar da Lahadi. Zaben 2015 na shugaban kasa shi ne mafi sarkakiya a tarihin demokuradiyyar Najeriya. Ku kasance tare da mu.

Za ku iya aiko mana da yadda al'amura suke wakana a yankunanku ta e-mail a hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook, ko ta whatsApp 08092950707 ko ta Twitter a @bbchausa.

*****Mun gode ku kasance tare da mu a ranar Talata domin ci gaba da sharhi a rubuce kai tsaye kan sakamakon zaben Najeriya. Mun gode. INEC ta ce sai gobe za a ci gaba da sanar da sakamakon zaben.

23:20 Shugaban hukumar zabe, INEC, Furofesa Attahiru Jega ya sanar da dage zaman ci gaba da karanto sakamakon zaben shugaban kasa har sai gobe Talata da 10 na safe.

23:16 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Akwa Ibom, ya ce an kada kuri'a a kananan hukumomi 31 na jihar. Inda jam'iyyar APC ta samu kuri'u 58,411 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 953,304.

Hakkin mallakar hoto AFP AP

23:09 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Plateau, Prof Emmanuel Chukwu ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 17, inda aka tantance masu kada kuri'a 1,076,833. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 429,140 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 549,615.

22:56 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Imo ya sanar da cewa an gudanar da zabe a kananan hukumomi gaba daya a fadin jihar. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 133,253 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 559, 185.

22:45 Bayan hutun sa'a daya a yanzu an koma sanar da sakamako. Amma kuma an cewa babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a Akwa Ibom ya je ya gyara alkalumansa akwai kuskure.

21:45 An dakatar da sanar da sakamakon zabe. An tafi hutu na minti 10 kafin a koma sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.

21:41 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Abia Prof. Benjamin ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 17 inda aka tantance masu kada kuri'a 442,538. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 13,394 inda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 368,303.

21:35 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Anambra Prof. Chigozie ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 21 inda aka tantance masu kada kuri'a 774,430. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 17, 926 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u660, 762.

21:27 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Kaduna Prof Kaura ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 23 inda aka tantance masu kada kuri'a 1,746,031. Jami'iyyar APC ta samu kuri'u 1,127,760 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 484,085.

21:22 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Kwara Prof. Akonji ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 16 ina aka tantance masu kada kuri'a 489,360. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 302,146 sai kuma jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 132,602.

21:16 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Katsina, Prof Amin ya sanar da cewa an gudanar da zabe a kananan hukumomi 34 inda aka tantance masu kada kuri'a 1,578,646. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 1,345,441 a yayinda PDP ta samu kuri'u 98, 937.

21:10 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Jigawa Prof. James ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 37 na jihar inda aka tantance masu kada kuri'a 1,153,428. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 885,988 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 142,904.

Hakkin mallakar hoto

21:00 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Kano, Prof Mohammed ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 44 inda aka tantance masu kada kuri'a 2,364,434. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 1, 903, 999 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 215, 779.

20:56 A jihar Gombe, a zaben shugaba kasa, jam'iyyar APC ta samu kuri'u dubu dari uku da sittin da daya da yan kai, yayin da jam'iyyar PDP ta samu kuri'u dubu casain da shida da yan kai. A zaben majalisar dattawa a jihar ta Gombe, jam'iyyar APC ta samu kujeru biyu, yayinda jam'iyyar PDP ta samu kujera daya.

20:54 Bayanan da muke samu daga wakilinmu Ishaq Khalid a Bauchi na nuna cewa an bayyana sakamakon zabe a jihohin Pilato. A zaben shugaban kasa jam'iyyar PDP ta samu kuri'u dubu dari biyar da arbain da tara da 'yan kai, yayinda jam'iyyar APC ta samu kuri'u dubu dari hudu da ashirin da tara da yan kai. A zaben majalisar dattawa, jam'iyyar PDP ta lashe dukkan kujeru uku na majalisar dattawan jihar, ciki har da gwamnan jihar mai ci yanzu Jonah Jang wanda ya lashe kujerar majalisar dattawa ta arewacin jihar Pilato.

20:45 Za a soma sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, bayan da shugaban INEC, Attahiru Jega ya koma cikin zauren tattara sakamako a Abuja

20:20 Mintuna 20 ana jiran shugaban hukumar INEC, Attahiru Jega domin a ci gaba da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a cibiyar tattara bayanai kan zaben da ke Abuja. Tun da farko Prof Jega ya yi alkwarin cewa za a ci gaba da sanar da sakamakon da karfe 8 na dare agogon Najeriya.

20:13 Gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi ya kafa dokar hana fita a birnin Fatakwal bayan zanga-zangar da ta biyo bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa dokokin tarayya.Dokar ta soma aiki ne daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe. Gwamnatin jihar ta ce ta dauki matakin ne domin kauce wa rikici sakamakon yanayin da ake ciki a siyasar jihar.

Image caption Manyan 'yan takarar da ke hamayya

19:56 Hukumar zabe a jihar Lagos ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a jihar Lagos, inda jam'iyyar APC ta Janar Muhammadu Buhari ta samu nasara da kuri'u 792,460 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 632,327.

19:47 Hukumar zabe ta kasa INEC ta kafa kwamiti da zai binciki zargin magudin zabe a jihar Ribas. INEC ta tura tawaga ta mutane uku domin duba korafin 'yan jam'iyyar APC a kan cewar jam'iyyar PDP ta yi aringizon kuri'u.

19:40 Hukumar zabe a jihar Kaduna ta ce jam'iyyar APC ce ta lashe zaben shugaban kasa da kuma kujerun 'yan majalisar dattijai biyu da na 'yan majalisar wakilai 11. A yayinda PDP ta samu kujerar dan majalisar dattijai daya da kuma na 'yan majalisar wakilai biyar.

18:40 Masu sa'ido na kasashen waje, sun yaba da yadda Najeriya ta gudanar da zaben shugaban kasar da na 'yan majalisar dokokin tarayya, duk da irin kalubalen da aka samu a wasu wuraren. Kungiyar National Democratic Institute NDI ta Amurka, da kuma tawagar kungiyar tarayyar Turai, sun yaba da yadda hukumomin kasar da al'ummarta suka taka rawar a zo a gani wajen sauke nauyin da ke kansu ya zuwa yanzu.

18:34 Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun gargadi mahukunta da 'yan siyasa a Najeriya da su guji yin katsalandan ga sakamakon babban zaben kasar. Wasu alamu da suke gani na yunkurin wasu shugabanni ko 'yan siyasa na yin kumbiya-kumbiyar sauya sakamakon zabe a cibiyoyin da ake tattara sakamakon zabe na matakan karshe.

18:19 An harba barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zanga magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari a birnin Fatakwal na jihar Ribas inda suke zargin an tafka magudi tare da yin aringizon kuri'u.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zanga-zanga a birnin Fatakwal

18:09 Ana zaman jiran sakamakon zaben shugaban kasa a jihohi 28 na Najeriya. A halin yanzu dai wasu gwamnoni kamarsu Mu'azu Babangida Aliyu na jihar Niger da Saidu Usman Dakingari sun sha kashi a kokarinsu na neman zaman sanatoci a kasar.

16:15 Shugaban hukumar zaben Najeriya, Furofesa Attahiru Jega ya bayyana cewa an dage zaman sanarda sakamakon zabe har sai karfe 8 agogon Najeriya. A wannan lokacin an samu karin sakamako daga jihohin kasar da dama.

16:10 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Nasarawa, Prof Abdulmumin Rafindadi ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 13 inda aka tantance masu kada kuri'a 562,959. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 236,838 sai kuma jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 273,460.

16:04 Yanzu kuma sai sakamakon zabe na jihar Nasarawa

16:02 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Oyo, Prof. Ayobami Salami ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 33 na jihar inda aka tantance masu kada kuri'a su 1,073,849. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 528,620 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 303,376.

15:55 Yanzu kuma sakamako daga jihar Oyo

15:50 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, Prof Micheal Foborode ya ce an kada kuri'a a kananan hukumomi shida inda aka tantance mutane 344,056. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 146,399 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 157,195.

15:43 Yanzu kuma sai sakamakon zabe a Abuja babban birnin kasar.

15:41 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Ondo, Prof Olusola Oyewole ya ce an gudanar zabe a kananan hukumomi 18 sannan an tantance mutane 618,040. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 299,889 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 251,368.

15:35 Yanzu kuma sai sakamakon zabe a jihar Ondo

15:30 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Osun, Prof. Isaac Asuzu ya ce mutane 683,169 aka tantance domin kada kuri'a a kananan hukumomi 30 na jihar. Jami'iyyar APC ta samu kuri'u 383,603 sai kuma jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 249,929.

15:26 Yanzu kuma sai jihar Osun.

15:25 Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza ya ce gwamnan jihar Kebbi, Sa'idu Usman Dakingari ya fadi zabe kujerar dan majalisar dattijai a jihar. Kuma jam'iyyar APC ce ta lashe galibin kujerun 'yan majalisa a jihar.

15:22 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Kogi Prof Adikwu ya ce an tantance mutane 476,839 domin kada kuri'a a kananan hukumomi 16. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 264,851 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 149,987.

15:13 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Enugu, Prof. Hilary ya ce mutane 616,112 aka tattance domin kada kuri'a a kananan hukumomi 17 a cikin jihar. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 14,157 sai kuma jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 553,003.

15:05 Yanzu kuma sai sakamakon zaben jihar Enugu.

15:00 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Ogun Prof. Duro Oni ya sanarda cewa an gudanar da zaben shugaban a kananan hukumomi 20 na jihar. Mutane 594,975 ne aka tantance domin kada kuri'a. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 308,290 a yayinda PDP ta samu kuri'u 207,950.

14:55 Yanzu kuma sai jihar Ogun

14:50 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Ekiti, Prof. Adeniyi Daramola ya sanarda cewa a gudanar da zabe a kananan hukumomin 16 inda jam'iyyu 14 ne suka fafata inda mutane 323,739 suka kada kuri'a. Jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 176,466 sai kuma jam'iyyar APC ta samu kuri'u 120,331. AA:94, ACPN: 534, CPP:330 ,HDP:94, KOWA:108, NCP:377, PPN:388, UDP:60, UPP:145.

Image caption Manema labarai a Abuja wajen tattara sakamakon zabe

14:38 Za a soma sanarda sakamakon zaben shugaban kasa na jihar Ekiti sannan sai Enugu sai kuma Ogun.

14:29 Sakamakon zabe daga jihar Kaduna a arewacin Najeriya, jam'iyyar APC ta lashe kujerun majalisar dattijai biyu a yayinda PDP ta samu kujera daya daga kudancin kasar. Sulaiman Uthman Hunkuyi ya kayarda tsohon gwamnan jihar Sanata Ahmed Muhammed Makarfi. A yayinda Comrade Shehu Sani ya doke Sanata Ahmed Aruwa. Sai kuma Danjuma Tela La’ah ya lashe kujera daga kudancin Kaduna.

14:20 An kammala tattara sakamakon zabe a jihar Oyo, inda jam'iyyar APC ta lashe kujerun 'yan majalisar datijjai uku da kuma na 'yan majalisar wakilai 12, sai kuma jam'iyyar PDP ta samu kujerar majalisar wakilai daya da kuma jam'iyyar Labour ta samu kujera daya, in ji wakilinmu Umar Shehu Elleman a Lagos kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

14:15 Mazauna birnin Kano sun shaida mana cewar mutane ba su fito kan tituna ba a birnin Kano. Bankuna sun kasance a rufe.

14:07 Wakilan jam'iyyar APC a wajen tattara sakamakon su ne Sanata Adeleke Olurunnimbe Mamora da kuma Dr Hakeem Baba Ahmed, a yayinda wakilan jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya su ne Elder Godsday Orubebe and Dr Bello Fadile. A cikin zauren akwai 'yan jarida da masu sa'ido kan zaben daga kasashen waje da kuma cikin gida.

14:00 Shugaban hukumar zabe, Furofesa Attahiru Jega ya shigo cikin zauran bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja babban birnin Najeriya

13:56 Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun gargadi mahukunta da 'yan siyasa a Najeriya da su guji yin katsalandan ga sakamakon babban zaben kasar. Cikin wata sanarwar hadin-gwiwa sun ce kawo yanzu dai babu wata shaida ta da nuna cewa a zahiri an yi magudi a matakan zabe a rumfunan zabe.

Image caption Zauren da ake tattara sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja

13:51 Tun karfe 12 na rana agogon Najeriya, hukumar zabe ta yi alkawarin soma bayyana sakamakon zabe a hukumance a cibiyarta a Abuja. Amma har zuwa karfe 1 da minti 52 ba a ji duriyar shugaban hukumar Furofesa Attahiru Jega ba.

13:40 A jihar Niger kuma hukumar zaben kasar reshen jihar ta sanarda cewa gwamna Mu'azu Babangida Aliyu ta fadi zaben kujerar majalisar dattijai, inda David Umaru na jam'iyyar APC ta lashe zaben.

13:31 A jihar Oyo da ke kudu maso yammacin kasar ma, jam'iyyar APC ce ta samu nasarar lashe kujerun majalisar dattawa uku; da kuma na majalisar wakilai 12 daga cikin 14 da ake da su a jihar. Ita kuma PDP ta samu kujera daya na majalisar wakilai a jihar ta Oyo.

13:25 Wakilinmu na Lagos, Umar Shehu Elleman ya ce an kammala tattara sakamakon zaben shugaban kasa a duka kananan hukumomin da ke jihar ta Lagos. A cewarsa, hukumar zabe a jihohoni Oyo da kuma Ekiti sun kammala tattara sakamakon.

Hakkin mallakar hoto INEC
Image caption Ana jiran shugaban INEC ya soma sanarda sakamako

13:16 Hukumar zabe a jihar Katsina ma ta sanarda cewajam’iyyar ta APC ta samu nasara a dukkanin zabukan shugaban kasa, da na majalisun dattijai da na wakilai a jihar

13:14 Wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya ce ajihar Jigawa jam’iyyar APC ta samu kuri’u 885,988, yayin da PDP kuma ta samu kuri’u 143,904 a zaben shugaban kasa kamar yadda hukumar zabe INEC ta sanarda. Sannan jam’iyyar ta APC ta kuma samu nasarar lashe kujerun 'yan majalisar dattijai uku daga jihar.

13:10 Hukumar zaben Najeriya reshen jihar Sokoto ta ce gwamnan jihar, Aliyu Magatakarda Wammako, ya lashe kujerar majalisar dattawa ta Sokoto ta arewa a karkashin jam'iyyar APC. Wakilinmu na Sokoto, Haruna Shehu Tangaza ya ce INEC din ta ce dukkan 'yan takarar jam'iyyar APC ne suka lashe kujerun majalisar dattawa da na wakilai a jihar.

13:06 Abin da hakan ke nufi shi ne Gwamna Rabiu Kwankwaso ya zama Sanata a mazabar dan majalisar dattijai a Kano ta tsakiya. Sannan kuma Sanata Bello Hayatu Gwarzo wanda ya shafe shekaru 16 a majalisar dattijai ya fadi zabe a karon farko tun maidoda mulkin demokuradiyya a 1999.

Image caption Karamar cibiyar tattara sakamakon zabe a Lagos

13:03 Hukumar zabe a jihar Kano ta ce jam'iyyar APC ta lashe kujerun 'yan majalisar dattijai uku da kuma na 'yan majalisar wakilai 24. Sannan kuma jam'iyyar APC ce ta lashe zaben shugaban kasa a jihar ta Kano.

13:00 Tun karfe 12 na rana agogon Najeriya muke jiran shugaban hukumar zaben kasar - INEC, Furofesa Attahiru Jega domin ya soma sanarda sakamakon zabe a cibiyar tattara sakamakon da ke Abuja amma bayan sa'a guda har yanzu babu bayanai daga INEC din.