An fitar da sakamakon Adamawa, Bauchi, Gombe, Taraba

Image caption Jam'iyyar APC ce ta lashe jihohin Bauchi da Gombe da Adamawa, yayin da PDP ta lashe Taraba

Hukumomin zaben jihohin Bauchi da Adamawa da Taraba da Gombe sun fitar da sakamakon zaben shugaban kasa.

A jihar Bauchi, hukumar zaben ta ce jam'iyyar APC ta lashe zaben da kuri'u 931,598, yayin da jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 86, 085.

A jihar Adamawa, jam'iyyar APC ta lashe zaben da kuri'u dubu 374,701 yayin da jam'iyyar PDP ta samu kuri'u dubu 251, 664.

A jihar Gombe, jam'iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa da kuri'u dubu 361,425 yayin da jam'iyyar PDP ta samu kuri'u dubu 96,884.

A jihar Taraba, hukumar zaben jihar ta ce jam'iyyar PDP ce ta lashe zaben da kuri'u 310,805, yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 261,326