PDP ta tayar da yamutsi a wajen tattara sakamakon zabe

Image caption Orubebe ya so ya hargitsa taron

Wakilin jam'iyyar PDP a zauren tattara sakamakon zaben Najeriya, Elder Godsday Orubebe, ya kawo yamutsi a wajen taron sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja.

Yana mai cewa jam'iyyar PDP ba ta gamsu da rawar da shugaban INEC, Attahiru Jega ke taka wa ba.

Jim kadan bayan bude zaman tattara sakamakon sai 'yan PDP din suka tayarda hatsaniya.

Mr Orubebe ya ci karensa babu babbaka inda jami'an tsaro sun ki cewa komai a kai.

Sai dai duk da batancin da ya rika yi a kan shugaban hukumar INEC, Jega bai ce uffan ba.

Wakilan jam'iyyar APC sun yi masa magana amma ya rika neman su da fada.