Najeriya: An bukaci a sake zabe a jihar Rivers

Image caption Masu layin kada kuri'a a Najeriya

A jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Nigeria, wasu jam'iyyun siyasa 14 sun gudanar da zanga-zangar lumana a ofishin hukumar zabe a jihar domin nuna rashin amincewarsu da zaben da aka yi.

Masu zanga-zangar da suka hada da magoya bayan babbar jam'iyyar adawa ta APC, sun yi zargin cewa ba a yi zaben bisa doka da adalci ba.

A saboda haka masu zanga zangar suka bukaci a gudanar da sabon zabe a jihar.

Hukumar zaben ta Najeriya ta ce za ta binciki wannan zargi.

A ranar zaben, gwamnan jihar ta Rivers, Mista Rotimi Amaechi ya yi zargin cewa ba a kai takardun shigar da sakamakon zabe a wasu runfunan zaben ba, lamarin da yasa ya ce shi da wasu magoya bayansa ba zasu kada kuri'a ba.