Barkewar cutar Ebola: Ba aiki, ba kwallo

Kasar Saliyo ta fi kowace kasa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon cutar Ebola.

Duk da dai cewar ana samun raguwar yaduwar cutar, makarantu suna rufe, sannan ana shawartar mutane su jinkirta yin aure kuma an hana wasan kwallon kafa.

Ga bayanai daga 'yan Saliyo a kan yadda cutar ta shafi rayuwarsu a halin yanzu.

Hakkin mallakar hoto Red cross

Kanwar Alice Mansaray ta rasu a sanadiyyar cutar Ebola. Babanta ma ya kamu da cutar amma ya warke. An killace gidansu domin kula da su. Ta ce '' komai ya tsaya cik tun farkon yaduwar cutar Ebolan. Bama iya zuwa makaranta kuma yanzu ma ba zan iya ziyartar kawayena ba.''

Hakkin mallakar hoto Red Cross

Aminatta Grant ta na zaune ne a wurin da aka killace da wasu mutane fiye da hamsin da suka kamu da cutar. Mutane biyu sun mutu a sanadiyar cutar sannan wata matashiya tana kwance a asibiti. Ta ce, '' a da mutane da dama sun dogara da mu. Amma a yanzu, ba za ma su taba abincin gidan da aka killace mu ba. Suna kyamar mu, kuma suna kiran mu Ebola. Ko masallaci ma ba ma iya zuwa yanzu.''

Hakkin mallakar hoto Red Cross

Tamba Lebbie tana da mukamin kofir a rudunar sojin Saliyo, inda yanzu take sanya ido a kan gidajen da aka killace na masu cutar. Ta ce, ''ina zama fiye da sati biyu a kowana gida na wadanda aka killace kuma ina jin tattaunawa. Ina jin dadin wannan aiki, domin a da zama kawai nake yi a bariki.''

Hakkin mallakar hoto Red Cross

Haja Kargbo tana saye da sayarwa ne a kasuwa lokacin da ta kamu da cutar Ebola. A yanzu tana aikin sa kai ne da kungiyar agaji ta Red Cross, a inda ta ke taimakawa wajen gano wadanda suke nuna alamun cutar. Ta ce, ''ba zan iya biyan kungiyar Red Cross abin da suka yi min na maganin Ebola ba. Amma dai zan iya taimaka musu.''

Hakkin mallakar hoto RedCross

Chernor Kamara dalibi ne mai nazarin harkokin kasuwanci a birnin Freetown. An rufe makarantarsu saboda haka yanzu yana aiki ne a matsayin wakilin al'umma a kungiyar agaji na Red Cross. Ya ce, ''yanzu babu lokacin karatu. Amma a wani bangaren kuma, rayuwa ta ta inganta. A da ba na yin komai bayan makaranta, amma a yanzu na samu wata kwarewa a wani fanni na daban inda nake ganawa da mutane.''

Hakkin mallakar hoto Red Cross

Sumaile Lamboi a da dalibi ne mai koyon aikin likita kafin bayyanar Ebola. Amma a yanzu yana aiki ne tare da masu binne wadanda suka rasu. Ya ce, ''ina so na taimakawa kasata a wannan lokaci na annoba. Nasan abu ne mai hadari amma kuma aikina ne.'' Ya ce, ''komai ya tsaya cik yanzu, a da ina kallon wasan kwallon kafa a duk karshen sati saboda ni dan Arsenal ne amma a yanzu ba za mu iya yin hakan ba.''

Hakkin mallakar hoto Red Cross

Mawa Kamara tana sayar da tufafi irin wadanda aka fi sani da 'lappa' a kasuwar Freetown amma ta ce ba a sayen kayan sosai yanzu saboda dokar hana fita da yamma da aka saka. Ni Musulma ce kuma bisa al'adarmu muna gaisawa da juna, amma a yanzu ba ma yi, ba a aure-aure da sauran taruka.''

Hakkin mallakar hoto Red Cross

Mohamed Bangura dalibi ne a fanin kasuwanci a Freetown. Ya ce, ''bana jin dadi saboda an rufe makaranta. Kuma babu damar walwala kamar wasanni. A da mukan taru da abokai muna hira da sauransu amma yanzu an hana taro, kuma ba zan iya zuwa wajen budurwata ba saboda babu abin hawa da dare kuma yan sanda sun tsananta aikin tsaro.''

Hakkin mallakar hoto Red Cross

A da Zainab Bangura tana sayar da garin flawa ne a kauyen Hamilton da ke bakin teku, amma yanzu sam-sam komai ya tsaya tun bayyanar cutar Ebola, da kyar ta ke iya ciyar 'ya'yanta uku. Ta ce, ''abubuwa sun yi tsanani yanzu, dole na dage na yi aiki sosai.''