Jonathan ya taya Buhari murnar lashe zabe

Image caption Janar Buhari da Shugaba Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan ya kira Janar Muhammadu Buhari ya kuma taya shi murnar lashe zaben shugaban kasa.

Mr Jonathan ya amsa shan kaye a zaben da suka fafata tsakaninsu.

Bayanai sun nuna cewa Shugaba Jonathan ya kira Janar Buhari ta wayar salula na tsawon minti hudu inda ya taya murnar wannan nasarar.

Tuni aka soma bukukuwa a fadin kasar domin nasarar Janar Buhari musamman a arewacin kasar.