Kai Tsaye:Sakamakon zaben shugaban Najeriya

Latsa nan domin sabunta shafin

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Najeriya sun shafe daren jiya suna kallon sakamakon zaben shugaban kasa a talabijin.

Barka da zuwa shafin BBC Hausa kai tsaye a kan sakamakon zaben shugaban kasa da aka fafata tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan na PDP da Janar Muhammadu Buhari na APC.

Za ku iya aiko mana da ra'ayoyinku ta e-mail hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook, ko ta whatsApp 08092950707 ko ta Twitter a @bbchausa.

22:21 Shugaban hukumar zabe INEC, Prof Attahiru Jega ya sanar da cewa an kamalla tattara sakamakon zaben shugaban kasa a jihohi 36 da kuma Abuja.

22:20 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Borno, Prof. Yacanami Karta ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 27 inda aka tantance masu zabe 544,759. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 473,543 ta samu kuri'u a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 25,640.

17:45 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Delta, Prof. Bolaji ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 25 inda aka tantance masu zabe 1,350,914. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 48,910 ta samu kuri'u a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 1,211,405.

17:34 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Sokoto, Prof. Abubakar ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 23 inda aka tantance masu zabe 988,899. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 671,926 ta samu kuri'u a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 152,199.

17:04 Saura jihohi uku:

Editan sashin Hausa na BBC, Mansur Liman ya ce sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohin Borno da kuma Sokoto za su kawar da sakamakon da Goodluck Jonathan zai samu daga jihar Delta na kudancin kasar.

A cewarsa, Janar Buhar na APC na kan hanyar lashe zaben shugaban kasa.

Hakkin mallakar hoto AP

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Magoya bayan Janar Buhari sun soma bukukuwar murnar nasararsa

17:00 Muna sanar da ku cewa, shirinmu na daren yau zai kasance na tsawon awa guda ne. Za a fara daga karfe takwas da rabi na dare zuwa tara da rabi na dare. Za kuma mu mayar da hankali ne kacokan kan sakamakon zaben shugaban kasa a Najeriya.

16:08 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Taraba, Prof. Mohammed ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 16 inda aka tantance masu zabe 638,578. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 261,326 ta samu kuri'u a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 310,800.

15:55 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Edo, Prof. Osaze ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 18 inda aka tantance masu zabe 599,166. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 208,469 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 286,869.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Miliyoyin 'yan Najeriya suna jiran sakamakon zaben

15:42 Dan takarar adawa ta APC, Muhammadu Buhari na kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasa.

Sauran jiha daya da ake gannin cewar Shugaba Goodluck Jonathan ne zai iya lashewa watau jihar Delta. A yanzu Janar Buhari na da kuri'u 13,763,769 a yayinda shugaban Jonathan ya samu kuri'u 10,866,249.

Ana jiran sakamako daga jihohin Borno da Sokoto inda jam'iyyar APC ke da rinjaye.

15:20 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Yobe, Prof. Ibrahim ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 17 inda aka tantance masu zabe 520,127. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 446,265 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 25,526.

15:10 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Bauchi Prof. Farouk ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 20 inda aka tantance masu zabe 1,094,069. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 931,598 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 86,085.

14:59 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Benue, Prof. Makuya ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 23 inda aka tantance masu zabe 754,634. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 373,961 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 303,737.

14:37 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Kebbi, Prof. Ahmadu ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 21 inda aka tantance masu zabe 792,817. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 567,883 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 100,972.

14:30 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Zamfara, Prof. Abdullahi ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 14 inda aka tantance masu zabe 875,049. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 612,202 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 144,833.

14:15 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Adamawa, Prof Jerry ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 21 inda aka tantance masu zabe 709,993. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 374,701 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 251,664.

13:35 Bayan sanar da sakamakon zabe a jihohi 25 da kuma Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, jam'iyyar adawa ta APC ce ke kan gaba inda ta bai wa jam'iyyar PDP tazarar kuri'u fiye da 500,000. Ana jira sakamakon zaben shugaban kasa daga jihohin Zamfara, Delta, Sokoto, Kebbi, Adamawa, Taraba da sauransu.

13:05 An tafi hutu na minti 30 kafin a ci gaba da sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja.

13:00 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Rivers, ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 23 inda aka tantance masu zabe 1,643,409. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 62,238 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 1,487,075.

Image caption Mutane na sauraron alkaluman zaben shugaban kasa a Kano

12:50 Shugaban INEC, Attahiru Jega ya ce babu inda ake gudanar da zabe ba tare da 'yan matsaloli ba, a don haka babu wata gamsashiyyar hujjar da za ta sa a soke zaben shugaban kasa a jihar Rivers.

12:35 Babbar jami'ar kula da zaben shugaban kasa a jihar Cross Rivers, Prof Ekpo ta ce an gudanar da zabe a jihohi 18 inda aka tantance masu kada kuri'a 500,577. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 28,368 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 414,863.

12:24 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Gombe, Prof Ibrahim ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 11 inda aka tantance masu kada kuri'a 515,828. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 361,245 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 96,873.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jega cikin tsanaki ya ja kunen dan PDP Godsday Orubebe

12:18 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Bayelsa Prof. Joseph ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 8 inda aka tantance masu kada kuri'a 384,789. A cewarsa, Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 5,194 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 361,209.

12:10 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Lagos Prof. Adewole ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 20 inda aka tantance masu kada kuri'a 1,678,754, inda jam'iyyar APC ta samu kuri'u 792,460 sai kuma jam'iyyar PDP wacce ta samu kuri'u 632,327.

11:58 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Niger Prof. Ambali ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 25 inda aka tattance masu kada kuri'a 933,607. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 657,678 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu 149,222.

11:52 Babban jami'in kula da zaben shugaban kasa a jihar Ebonyi Prof. Ahaneku ya ce an gudanar da zabe a kananan hukumomi 13 inda aka tattance masu kada kuri'a 425,301. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 19,518 a yayinda jam'iyyar PDP ta samu 323,653.

11:45: An ci gaba da karanto alkaluma, Prof Jega bai nuna wata damuwa ba kan wannan zargin da 'yan PDP suka yi masa.

Hakkin mallakar hoto NTA
Image caption Yadda Orubebe ya tayar da hatsaniya

11:31 Hatsaniya a cikin zauren tattara sakamakon, Mr Orubebe ya na cikin karensa babu babbaka, jami'an tsaro sun ki cewa komai a kai.

11:26 Wakilin jam'iyyar PDP a zauren tattara sakamakon zabe Elder Godsday Orubebe ya nemi ya ta da taron, inda ya ce jam'iyyar PDP ba ta gamsu da rawar da shugaban INEC, Attahiru Jega ke taka wa ba.

11:18 An bude zauren sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a cibiyar tattara sakamako a Abuja inda shugaban INEC Attahiru Jega ke kan babbar kujera.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Miliyoyin 'yan Najeriya na lissafa yawan kuri'u a wayarsu

11:10Alkaluma

A halin yanzu tsohon shugaban mulkin soji Muhammadu Buhari ya samu kuri'u fiye da shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

  • Janar Buhari na jam'iyyar APC ya lashe kuri'u : 8,520,436
  • Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP: 6,488,210

11:00 'Yan Najeriya sun kwana suna tunanin yadda za ta kaya game da sakamakon zaben shugaban kasar. Shugaban hukumar zaben Attahiru Jega ya ce za a ci gaba da sanar da sakamakon zaben a yau da karfe 10 na safe. A jiya dai an sanar da sakamakon zaba a jihohi 19 da kuma birnin tarayya Abuja. A yanzu ana jiran sakamakon zabe na jihohi 17.