Amazon ya kirkiri na'urar odar kaya cikin gida

Hakkin mallakar hoto AMAZON
Image caption Kamfanin Amazon ya yi fice a duniya

A wani yunkuri na jan hankalin masu sayayya daga cikin gida, katafaren kamfanin Amazon ya kaddamar da wata na'ura da zata iya yin odar kaya irinsu hodar wanke- wanke da kuma reza

Za a iya makala madannin na'urar 'Dash' ga kayayyakin cikin gida, sannan idan aka danna na'urar za ta ta yiwo odar kaya.

Masu amfani da tsarin Prime na kamfanin Amazon ne kadai za su iya cin moriyar wannan sabuwar fasaha

Katafaren kamfanin Amazon dai a baya bayan nan ya maida hankali wajen gyara tsarin odar kayansa ta yadda zai kasance cikin sauri

Wannan tsari na Prime a yanzu na bayar da garantin kai kayayakin da ake bukata cikin sa'a guda kuma wannan tsari zai yi aiki a birane hudu na Amurka.

Sannan kamfanin na gwajin kai kayayyaki ta hanyar amfani da jirgi maras matuki

A ranar Litinin, kamfanin ya kaddamar da hanyar Amazon Home Services wacce zata bai wa kwastomomi damar odar ayyuka na kwararru kamar su mai gyaran kwamfuta.

Da fari dai wasu sun dauka wannan sabon tsari da Amazon ya kirkiro da shi ba gaskiya ba ne.

Kuma koma bayan an tabbatar da tsarin a matsayin na zahiri, wasu na tababar yadda abin yake