Za mu kawar da Boko Haram — Buhari

Hakkin mallakar hoto
Image caption Buhari ya bai wa Jonathan tazarar kuri'u fiye da miliyan biyu

Zababben shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa za ta "zage damtse" domin murkushe ayyukan kungiyar Boko Haram.

A jawabinsa a Abuja jim kadan bayan da hukumar zaben Nigeria ta ba shi takardar shaidar lashe zaben shugaban kasa, Janar Buhari ya ce "Boko Haram za ta san karfinmu na kawar da ita."

Ya kara da cewar "Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen tattabar da mun samu galaba a kan 'yan ta'adda."

Kungiyar Boko Haram ta kashe a kalla mutane 20,000 sannan ta tursasa wa fiye da miliyan uku barin muhallansu, abin da ya jawo aka yi ta Allah-wadai da shugaba Jonathan saboda gazawarsa wajen shawo kan matsalar.

Tsohon shugaban mulkin sojan ya yi yakin neman zabensa a matsayin sabon dan siyasa wanda yake da niyyar kawo gyara a harkokin siyasar kasar.