Shugabannin duniya na taya Buhari murna

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama da Firai-ministan Birtaniya, David Cameron sun kasance a sahun gaba, wajen taya zababben shugaban Nigeria Janaral Muhammadu Buhari murna tare da jinjina wa shugaban kasar mai barin-gado, Goodluck Jonathan bisa dattakun da suka ce ya nuna.

Harwa yau, shuwagabannin sun bayyana aniyyarsu na aiki tare da Janaral Muhammadu Buharin.

Shima a jawabin da ya yi bayan ya karbi takardar shaidar zaben sa, Janaral Muhammadu Buhari ya yi wa Shugabannin godiya ta musamman saboda tsayawarsu da kuma goyan bayan da suka nuna wajen ganin cewa an gudanar da zaben lami lafiya.

Kuma ya tabbatar musu da cewa Nigeria zata taka mahimmiyar rawa wajen yaki da ta'addanci da kuma wasu matsloli na bai-daya da suka hada da yaki da miyagun kwayoyi da canjin yanayi da zambar kudi da cututtukan da ake yadawa da kuma wsau batutuwan da suke bukatar duniya ta dauki mataki.