Amurka da Iran suna tattauna wa a kan nukiliya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wakilan manyan kasashen duniya na tattauna wa a kan shirin Iran na nukiliya

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya soma tattaunawa da takwaransa na kasar Iran Javad Zarif, yayin da ake cigaba da tattaunawa domin cimma yarjejeniya kan shirin nukliya na Iran.

Masu shiga tsakani na matukar kokarin ganin bangarorin sun cimma matsaya bayan da suka kasa cimma wa'adin da suka sa wa kansu.

Ana dai samun bayanai daban -daban daga wurin mahalatta taron.

Wasu daga cikinsu sun yi hasashen cewa za'a cimma matsaya nan bada jimawa yayin da wasu sun ce ke ganin da sauran rina a kaba .

Ministan harkokin waje na Faransa Laurent Fabius, ya ce "Ana samun cigaba a tattaunawar da ake yi sai dai yanzu ba mu kai matakin kamala tattaunawar cikin gaggawa ba."