'Yan tawaye sun kwace fadar shugaban Yemen

Image caption Militiamen seize Yemen presidential palace

'Yan tawaye a Yemen sun kwace iko da fadar shugaban kasar da ke garin Aden a kudancin kasar, bayan wani gagarimin hargitsi tun lokacin da shugaba Abd Rabbu Mansour Hadi ya arce a makon da ya gabata.

Mayakan sa kai 'yan Houthi da wasu dakarun sun isa fadar shugaban kasar a cikin motoci masu silke.

Rahotanni sun ce tun da farko wasu mutane dauke da makamai sun baro garin Aden da ke bakin ruwa.

A waje daya kuma ana ci gaba da gumurzu a cikin tsakiyar birnin tsakanin mayaka 'yan Houthi da kuma dakarun da ke biyayya da Shugaba Abd Rabbu Mansour Hadi.

A bangaren arewacin kasar ta Yemen kuma da ke kusa da kan iyakar Saudi Arabia inda nan ne cibiyar 'yan tawayen Houthi, an samu rahoton kashe wani sojan Saudiyya sannan kuma aka raunata wasu da dama.