Boko Haram: Turkiyya za ta bai wa Kamaru makamai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram na kai hare hare Kamaru

Kasar Turkiyya za ta taimakawa Kamaru da kananan makamai da kuma wasu dabarun yaki da kuma samun bayanai domin hakan ya kara taimakawa dakarun Kamarun tunkarar yaki da ta'addanci masamman ma na kungiyar Boko Haram.

Wannan yunkurin na kasar Turkiyya ya biyo bayan izinin da majalisar dokoki ta baiwa Shugaban Kasa da ya rattaba hannu akan wasu yarjejeniyoyi da suka shafi batun tsaro.

Gabannin haka kuma wasu manyan jami'an kasashen biyu sun fara fadada huldar da ke a tsakaninsu a makon jiya, a birnin Ankaran Turkiyya karkashin sa hannu da su ka yi a kan yarjejeniyar da ta fuskanci batun tsaro.

Kamaru dai na daya daga cikin kasashen dake fama da hare haren Boko Haram