Cutar Sankarau: Mutane 45 sun mutu a Niger.

Image caption mutane 45 sun mutu a Niger sakamakon barkewar cutar Sankarau

Kimanin mutane 45 ne suka rasa rayukansu a jamhuriyar Niger bayan barkewar annobar cutar sankarau a kasar.

Bayanai sun nuna cewa kimanin mutane 345 ne suka kamu da cutar kuma mutane 45 ne suka mutu sakamakon ta.

Haka kuma, an samu barkewar cutar kwalara a kasar a inda sama da mutane 2000 suka kamu da cutar kuma tayi sanadiyar mutuwar mutum biyu kawo yanzu.

Hukumomin kasar dai na cewa suna kokarin kange cututtukan daga kara yaduwa.